COMA' PROJECT – Telegram
COMA' PROJECT
143 subscribers
579 photos
22 videos
1 file
54 links
Download Telegram
Yau ne ranar ƙarshe na kwana goma da ƴan Najeriya suka ɗauka 1-10 August nayin zanga-zangar tsadar rayuwa a ƙasar, a yau ɗin kuma ranar ƙarshe wasu ƴan Najeriya sun fito a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja domin cigaba da nuna ma gwamnati cewa sun gaji da ita.
Duk a cikin wannan tsadar rayuwar da ake ciki a Najeriya!

Wasu masu gidajen mai a ƙasar sun kara farashin litar man fetur.

shin ko menene dalilin su nayin hakan?

muna da kun ra'ayin ku
APC Kano State, expresses concern over diversion, rebranding Federal Government {APC President Bola Tinubu Government} Palliatives, threaten legal action against Kano State Government officials.
Al'umma sun gudanar da sallar nafila da addu'o'in neman saukin tsadar rayuwa a jihar Kano dake Najeriya.
APCn jihar Kano ta ce za ta dauki matakin shari’a kan zargin karkatar da Shinkafar da Gwamnatin Bola Tinubu ta bayar a raba a jihar.
''Zamu haɗa kai da masu kishin Arewa da attajiran yankin kamar Dangote, Abdul'aziz Yari da Kwankwaso domin nemarwa yankin mafita kan halin da yake ciki.''

Sanata Kashim Shettima
Mataimakin Shugaban Ƙasa a Najeriya.
An bawa jami'an tsaron ƴan sanda Mata damar sanya Hijabi ya yin fitowa aiki a jihar Kano dake Najeriya.
Zan tabbatar APC ta lashe zaben jihar Kano a 2027
Yadda aka yi hada-hadar kudaden waje zuwa Naira a kasuwar sauyin kuɗi ta Wapa da ke jihar Kano.
#premierradio #premierkano #premierradiong
Babu wanda aka kashe lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da a kayi a Kano.
Ya halatta ayi daurin aure ta waya tsakanin mai bayarwa da mai karɓa.
The All Progressives Congress APC is preparing to convene a National Executive Committee {NEC} meeting in September, along with a Mid-Term Convention {Non-elective} scheduled to take place before the end of 2024.
I am delighted to announce you my nomination as Honourable Member, Representing Tarauni Local Government Area of Kano State 4th Republic Assembly and I am thrilled to be recognized among an esteemed group of individuals who have made significant contributions to the development of our great nation Nigeria.

Our inauguration will soon take place.

#StongerTogether

Hon. Mukhtar, ABDULLAHI COMA'
Member Representing Tarauni Local Government Area, Kano State.
4th Republic Assembly, YAN.
Albashi na a Majalisar Dattawa bai kai Miliyan ɗaya ba, sannan kuma ana bai wa Kowane sanata naira miliyan ashirin da ɗaya a kowane wata a matsayin kuɗin gudanar da ofis.
Majalisar tsofaffin shuwagabannin Najeriya, sun zargi ƴan Najeriya wanda sukai zanga-zangar tsadar rayuwa da yunƙurin sauya gwamnati a lokacin da suka gudanar da zanga-zangar, wanda hakan ya sanya majalisar kaɗa ƙuri'ar amincewa ga Bola Ahmed Tinubu a matsayin sa na shugaban ƙasar Najeriya, tare da nuna rashin ƙin yarda da duk wani yunƙurin sauyin gwamnati ba ta hanyar zaɓe ba.
A wanni kaɗan bayan da Ɗan Bello ya fitar da wani bidiyo na zargin cin hanci da rashawa akan Farfesa Hafsat GANDUJE {Matar Ganduje}, Kwa tsam gwamnatin jihar Kano ta fitar da sanarwa cewa cikin mutanen da sukai zanga-zangar tsadar rayuwa kwanakin baya an samu wasu daga cikin su sun shiga kotun jihar sun sace takardun shari'ar da ake ma Dr. Abdullahi Umar GANDUJE.
This media is not supported in your browser
VIEW IN TELEGRAM
Daga cikin tattaunawar da akai da Hon. Abdullahi Sidi Ali tsohon Ɗan takarar shugabancin matasa a jam'iyyar APC Arewa maso yamma
Rahotanni sun nuna cewa shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr. Abdullahi Umar GANDUJE, ya yi fatali da tayin da shugaban ƙasa Tinubu ya yi mashi na Ambasada a ƙasar da yake so a Afrika, Asiya ko Europe.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta jihar Kano ta bukaci ƴan takarar shugabannin ƙananan hukumomi su biya naira miliyan 10, Kansiloli su biya miliyan 5 a matsayin kuɗin fom na tsayawa takara wanda za'a gudanar ranar 30 ga watan Nuwamba 2024 a jihar.
A yammacin jiya Laraba 14 ga watan Agusta 2024. Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu da shugaban Ƙasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar aikin bututun iskar gas na Gulf of Guinea, tare da kara kulla dankantaka tsakanin kasashen biyu.